2014: Hodgson ba zai kara 'yan wasa ba

Image caption Hodgson ya kwantarwa da 'yan wasansa hankali

Kociyan Ingila Roy Hodgson, ya ce ba ya tsammanin zai kara sabuwar fuska a cikin tawagarsa dan buga gasar cin kofin duniya na 2014.

Hodgson yana da ragowar wasa da Denmark ranar 5 ga watan Maris kafin ya zabi tawagar 'yan wasa 30 wadanda za su Brazil.

Amma ya cire duk wata bazata da za a yi tsammanin zai yi don wasan , duk kuwa da lallasau a jere da Chile da Jamus suka yi.

Ingila dai ta fito gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa Poland a Wembley ranar 15 ga watan Octoba.

Karin bayani