Johnny na fatan zama Kociyan Saliyo

Image caption Johnny McKistry na nema zama kociya na din-din-din

Johnny McKinstry yana fatan za a nada shi kociyan Saliyo na din-din-din bayan ganawa mai ma'ana da ya yi da Hukumar Kwallon kafa ta kasar da kuma Ma'aikatar kula da wasanni.

McKinstry, an sa shi ya jagoranci Kungiyar kwallon kafa ta kasar na rikon kwarya a watan Aprilu.

Kociyan, ya kuma jagoranci tawagar a wasannin su uku na neman fitowa gasar cin kofin duniya 2014.

Kociyan ya ce alhakkin da ke wuyansa shine ya ja ragamar Kungiyar kwallon kafar ta Leone Stars zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a yi a Morocco a 2015.