Kofin Duniya : Uruguay ta cike gurbi

'Yan wasan Uruguay
Image caption Duk da matsawar da Suarez da Cavani suka yi wa Jordan sun kasa sa kwallo a raga

Uruguay ta zama kasa ta karshe da ta samu gurbin gasar wasan kwallon kafa ta duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Kasar ta samu wannan dama ne bayan da ta tashi ba ci, 0-0 a karawarta ta biyu da kasar Jordan a birnin Montevideo na Uruguay.

Daman a karawar farko Jordan ta sha kashi da ci 5-0 a gidanta.

Uruguay wadda itace ke matsayi na shida a gwanayen kwallon kafa a duniya ta dauki Kofin Duniyar a 1930 da 1950.

Haka kuma ta kai wasan kusa da na karshe a gasar ta karshe da aka yi a Afrika ta Kudu.

Jordan wadda ba ta taba zuwa gasar Kofin Duniya ba ita ce ta 70 a jerin gwanayen FIFA.

Karin bayani