Ayew zai yi jinyar makwanni takwas

Image caption Andre da kaninsa Jordan Ayew

Dan kwallon Ghana Andre Ayew zai yi jinyar makwanni takwas sakamakon rauni a gwiwarsa.

Dan shekaru 23 ya ji rauni ne lokacin wasan Ghana da Masar a ranar Talata.

Kungiyar a Faransa wato Marseille ta ce a ranar Litinin mai zuwa za a yi wa Ayew tiyata a gwiwarsa.

A lokacin wasan, Ghana ta sha kashi a hannun Masar daci biyu da daya amma kuma za ta Brazil saboda lallasa Masar din a Kumasi daci 6 da 1.

Karin bayani