Carrick ya sabunta yarjejeniyarsa a Man U

Image caption Moyes ya ce Carrick dan wasa ne gogagge

Dan wasan Manchester United, Michael Carrick, ya tsawaita kwantaraginsa a Old Trafford zuwa watan Yunin shekarar 2015, kuma yana da zabin ci gaba da kasancewa a kungiyar har gaba da haka.

A halin da ake ciki dai dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekaru 32, na yin jiyyar raunin da ya samu, wanda kuma ya dagule tun lokacin wasan da kungiyar ta doke Arsenal 1-0 a Gasar Premier ranar 10 ga watan Nuwamba.

Carrick ya burge kocin kungiyar, David Moyes, bayan da ya fito sau 10 a kakar wasa ta bana.

Moyes ya ce, "Dan wasan na daban ne kuma yana da gogewa wajen buga kwallo''.

Karin bayani