Mourinho ya soki shugaban alkalan wasa

Jose Mourinho
Image caption Mourinho ya ce,'' ina son in sani cewa ko mutane na ganin hakan abin da ya dace ne.''

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya soki shugaban alkalan wasan Premier Mike Riley saboda bai wa West Brom hakuri akan fanaretin da aka ba wa Chelsea ta ci su.

Mourinho yana ganin abin da Riley yayi bayan da kungiyoyin suka tashi 2-2 a Stamford Bridge ranar 9 ga watan Nuiwamba bai dace ba.

Mourinho yana mayar da martani ne bayan da kociyan West Brom Steve Clarke ya bayyana cewa shugaban alkalan wasan ya kirawo shi a waya ya bashi hakuri kan fanaretin da alkalin wasa ya ba Chelsea.

Saura mintuna kadan a tashi alkalin wasan Andre Marriner ya ba Chelsea fanareti suka rama aka tashi 2-2.

Karin bayani