Walcott zai koma taka leda

Image caption Theo Walcott

Theo Walcott zai buga wa Arsenal kwallo a karon farko cikin fiye da wattani biyu bayan da ya murmure daga ciwon ciki.

Walcott na tawagar da za ta fafata da Southampton a ranar Asabar.

Dan kwallon mai shekaru 24, tun a ranar 22 ga watan Satumba a wasan Arsenal da Stoke, rabon da ya taka wa kulob din leda.

Kocinsa Arsene Wenger ya ce "Theo gogaggen dan kwallo ne kuma muna bukatar gudunmuwarsa a Gunners".

Karin bayani