Tsohon kyaftin din Man United ya rasu

Bill Foulkes
Image caption Foulkes ya dauki kofin gasar lig ta Ingila hudu da na FA daya.Ya buga wa Ingila wasa sau daya a 1954.

Tsohon kyaftin din Manchester United Bill Foulkes da ya tsira a hadarin jirgin sama da 'yan wasan kungiyar suka yi a birnin Munich na Jamus a 1958 ya rasu.

Foulkes wanda ya rasu yana da shekaru 81, daya ne daga cikin matasan 'yan wasan da kungiyar ke ji da su a lokacin kociyanta Sir Matt Busby.

A ranar 6 watan Fabrairu na 1958 jirgin saman da yake dauke da 'yan wasan na Manchester United daga Belgrade ya fadi sakamakon rashin kyawun yanayi na zubar dusar kankara da iska bayan ya sha mai a filin jirgin Munich.

Mutane 23 ne suka rasu a lokacin da suka hada da 'yan wasa takwas da 'yan jarida takwas da wasu jami'an kungiyar bakwai.

Bayan hadarin ne Foulkes ya zama kyaftin din kungiyar ya kuma zama gagarabadau a kungiyar.

Haka kuma ya dauki Kofin Zakarun Turai a Wembley lokacin da Manchester United ta lallasa kungiyar Benfica ta Portugal da ci 4-1 a 1968.

Marigayi Foulkes ya shiga Manchester United a matsayin matashin dan wasa a watan Maris na 1950 kuma ya fara wasa a matsayin kwararre a watan Agusta na 1951.

Ya fara yi wa kungiyar wasa a karawarta da Liverpool a watan Disamba na 1952.

Foulkes ya bar Manchester United a watan Yuni na 1970 inda ya tafi aikin kociya a wasu kungiyoyi a Amurka da Norway