Torres zai yi wasa yau

Fernando Torres
Image caption Mourinho ya ce, Torres yayi atisaye da kungiyar ranar Lahadi da Litinin ba tare da wata matsala ba.

Dan wasan gaba na Chelsea Fernando Torres ya warke daga raunin da ya ji kuma zai buga wasan Chelsea da FC Basel na Zakarun Turai yau Talata.

Chelsea na bukatar tashi canjaras (draw) a wasan na rukunin Group E, ta tsallake zuwa zagaye na gaba na sili daya kwale(knockout).

Idan kuma kungiyar ta yi nasara za ta zama ta daya a rukunin ta tsallake zuwa zagayen na gaba a matsayin ta daya a rukunin.

Yayin da Torres ya warke shi kuma David Luiz ba zai je Switzerland din ba inda za su yi wasan saboda rauni.

FC Basel sun kawo karshen jerin nasarar da Chelsea take samu sau 29 a matakin rukuni na gasar bayan da suka ci ta 2-1 a wasansu na farko a Stamford Bridge.

Sauran wasannin Zakarun Turan na yau su ne: Arsenal v Marseille da Celtic v Milan da Steaua Bucharest v FC Schalke 04

Borussia Dortmund v Napoli da Zenit St Petersburg v Atl├ętico Madrid da FC Porto v FK Austria Vienna da Ajax v Barcelona