Hart ba zai bar City ba in ji Pellegrini

Joe Hart
Image caption Joe Hart golan Ingila yana son dawowa ganiyar sa

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya karyata rade radin da ake cewa Joe Hart zai bar kungiyar a watan Janairu idan an bude kasuwar sayar da 'yan wasa.

Hart, mai shekaru 26 bai samu buga wa kungiyar wasanni shida ba, sakamakon ajiye shi a benci, sai dai ana sa ran za a sa shi a wasan da kungiyar za ta kara da Viktoria Plzen a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba.

Pellegrini ya ce "a na ta yamadidin muna son sayen masu tsaron raga bakwai ko takwas duk babu kanshin gaskiya, kuma Joe hart zai ci gaba da buga wasa tare da mu."

Hart, ya rasa gurbinsa bayan kura kuren da ya dinga yi, musamman a karawar da sukayi da Chelsea a inda Fernando Torres ya sami damar zura kwallon da suka lashe City da ci 2-1 a karawar da sukayi a Stamford Bridge ranar 27 ga watan Oktoba.

Golan ya kama wasa a karawar da Ingila ta yi rashin nasara da ci daya mai ban haushi a hannun Jamus a ranar 19 ga watannan a wasan sada zumunci, kuma ya rasa gurbinsa a City bayan da Costel Pantilimon ya maye gurbinsa a raga.