Mutane 2 sun mutu a filin wasan Brazil

Brazil Accident
Image caption Filin wasan na daga cikin wanda za a buge wasan farko

Mutane biyu ne suka mutu a Brazil bayan wani karfen daga abubuwa masu nauyi ya fado a kansu yayin da suke aiki a filin wasa na Sao Paulo.

Filin wanda yana daya daga cikin filayen wasan da za a buga Gasar kwallon kafar duniya ta shekarar 2014 a cikinsu.

Wani babban jami'in hukumar kashe gobara ya ce an kira su agajin gaggawa lokacin da suka sami rahotan karyewar karfen daga abubuwa masu nauyi.

Filin wasan an sa masa ranar kammala shi a karshen Disamba, domin cimma yarjejeniyar Fifa.

Brazil ta ce za ta yi kokarin kammala gina filaye 12 da za su karbi bakuncin gasar kafin lokacin wasannin.