Zama daram a Tottenham - Villas-Boas

Andrea Villas Boas
Image caption Kocin ya ce zai kara kaimi domin daga kungiyar sama

Kocin Tottenham Andre Villas-Boas ya ce yana da tabbacin har yanzu mahukuntan kungiyar da 'yan wasa suna mara masa baya akan aikinsa.

Tottenham ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 6-0 a gasar Premier da suka kara a ranar Lahadi da ta gabata, kungiyar tana matsayi na tara a teburi, Arsenal da ke matsayi na daya ta bata tazarar maki takwas.

Tuni ake hangen cewa Kocin dan kasar Portugal zai iya zama mai horarwa na gaba da zai iya rasa aikinsa.

Sai dai kocin ya ce "ina da tabbacin cewa mahukuntan kungiyar da 'yan wasa suna tare dani, saboda haka zanci gaba da gudanar da aiki na tukuru."