United ta casa Leverkusen 5-0

Manchester United
Image caption Nasarar data samu itace ta farko da ta zura kwallaye da yawa a gasar kofin Turai a wasan waje

Manchester United ta yi laga laga da Bayern Leverkusen har gida da ci 5-0 a gasar cin kofin zakarun Turai.

United ta zura kwallayenta ta hannun Luis Antonio Valencia sai kwallon Emir Spahic da ya zura wa kansu da kansu, daga nan Jonny Evans da Chris Smalling da Luis Nani suka zura sauran kwallayen.

Sauran sakamakon wasanni

Shakhtar Donetsk 4 - 0 Real Sociedad Juventus 3 - 1 FC Copenhagen Real Madrid 4 - 1 Galatasaray Paris Saint Germain 2 - 1 Olympiakos RSC Anderlecht 2 - 3 Benfica CSKA Moscow 1 - 3 Bayern Munich Man City 4 - 2 Viktoria Plzen

Kungiyoyin takwas da suka sami kaiwa zagayen gaba sun hada da Man Utd da Real Madrid da PSG da Bayern Munich da Man City da Chelsea da Atl├ętico Madrid da Barcelona.