Arsene Wenger na dar-dar da Napoli

Arsene Wenger
Image caption Sai a zagaye na karshe na wasan rukunin za a san kungiyar da ta tsallake

Kociyan Arsenal Arsene Wenger ya ce wasan da kungiyarsa za ta yi da Napoli na zakarun Turai na da hadari.

Amma duk da haka ya ce za su gama aikinsu su ci gaba zuwa mataki na gaba na gasar.

Wenger ya ce wannan shi ne karon farko da ya ke ganin maki 12 bai isa kungiya ta tsallake zuwa mataki na gaba ba a gasar.

Ya ce abu ne mai wuyar gaske da ba za ka yarda da shi ba amma kuma tabbas haka yake.

Arsenal ta daya da tsiran maki uku tana da maki 12 a rukuninsu na Group F, amma har yanzu tana fuskantar kalubale a rukunin tsakaninta da Dortmund da Napoli.

Nasarar da Arsenal ta samu akan Marseille 2-0 ranar Talata, na nufin kungiyar za ta iya tsira muddin Napoli ba ta yi galaba a kanta da kwallaye uku ba a wasan da za su yi ranar 11 ga watan Disamba a Naples.

A wasansu na farko a Emirates Arsenal ta ci Napoli 2-0, amma duk da haka Arsenal na dari-dari.