Masar ta nada Gharib a matsayin koci

Egypt Team
Image caption Kocin nasaran Masar ta taka rawa a gasar cin kofin Afrika

Hukumar kwallon kafar Masar ta sanar da daukan sabon koci Shawki Gharib.

Gharib tsohon dan kwallon Masar mai wasa a tsakiya, ya maye gurbin Bob Bradley, bayan da ya kasa kai kasar shiga gasar cin kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a badi.

Kocin mai shekaru 54, kafin Masar ta bashi aiki, ya karbi raganar horadda kungiyar Ismaily a watan jiya.

Lokacin da yake ganiyar wasansa, ya lashe kofin nahiyar Afrika da Masar a shekarar 1986, ya kuma dauki kofin a mataimakin koci tare da Hassan Shehata a shekarun 2006 da 2008 da 2010.