Fifa bata da shirin dage kofin duniya

Brazil Accident
Image caption Karfen daukar kaya masu nauyi ne ya karye ya kuma fada wani sashin filin wasa

Fifa ta ce bata da shirin dauke gasar cin kofin duniya daga Brazil duk da samun koma baya da kasar tayi a kokarin daukar nauyin bakuncin gasar a badi.

Ma'aikata biyu ne dai suka rasu lokacin da wani karfen daga abubuwa masu nauyi ya fado, ya kuma lalata wani sashi na filin wasan Corinthians dake Sao Paulo.

Filin wasan na shirin karbar bakuncin 'yan kallo 65,000, kasa da kwanaki 200 masu zuwa.

Wani babban jami'in Fifa ya ce hukumar bata da wani shirin dage gasar daga kasar Brazil.

Tuni Brazil ta sanar da cewa tana fuskantar kalubale a kokarinta na kammala ayyukan filayen wasa 12 da za a gudanar da gasar a cikinsu.