''Tottenham ta samu kwarin guiwa''

Andre Villas-Boas
Image caption Villas-Boas, ya ce, ''na yi matukar farin ciki da nasarar da muka samu.''

Kociyan Tottenham Andre Villas-Boas ya ce nasarar da suka samu a wasan Europa 2-0 akan Tromso ta basu kwarin guiwa.

Tottenham ta sha kashi a hannun Manchester City 6-0 ranar lahadi kuma za ta karbi bakuncin Man United ranar Lahadin nan.

A don haka kociyan ya ce wannan nasara da suka samu a gasar ta Kofin Europa ta karfafa musu guiwa sosai.

Tottenham tana matsayi na tara a Premier da maki 20 a wasanni 12, a bayan Manchester United da maki daya.

Man United za ta fuskanci Tottenhan din bayan da ta yi gagarumar nasara a wasanta na zakarun Turai da ci 5-0 akan Bayern Leverkusen ranar Laraba.