Fulham ta raba gari da Martin Jol

Martin Jol
Image caption Tun a baya kocin ya ce baya tsoron a kore shi daga Fulham

Kungiyar kwallon kafa ta Fulham ta sallami kocinta Martin Jol, sakamakon rashin tabuka rawar gani a gasar Premier bana.

Jol, mai shekaru 57 ya fara kocin Fulham a watan Yunin shekarar 2011, kuma an sallame shi ne saboda rashin nasara a wasanni biyar da yayi a jere a gasar Premier, kuma kungiyar tana matsayi na 18 a teburin kungiyoyi 20.

Tuni kungiyar ta bada sanarwar ce wa mataimakin sa Rene Meulensteen zai maye gurbinsa ana rikwan kwarya.

Shugaban kungiyar Shahid Khan ya ce baza mu zura ido kungiyar bata kokari ba, magoya bayan kungiyar suna bukatar kocin da zai kai ta ga ci.