Munich ta lashe wasanni 39 a jere

Arjen Robben
Image caption Kwallon farko Turke ta doka ta dawo kafin ya maida ita raga

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta tsawaita yawan lashe wasanni 39 a gasar Bundesliga, lokacin da ta lashe Eintracht Braunschweig a ranar Asabar.

Arjen Robben shine dai ya zura kwallo ta farko data biyu a raga.

Bayern tana ja gaba a teburin Bundesliga da maki 38, ta baiwa Bayern Leverkusen mai biye da ita a teburi tazarar maki hudu.

Tun sanda aka take wasa Bayern Munich ce ta dinga taka kwallo a karawar da sukayi da kungiyar Eintracht Braunschweig wacce take matsayi na karshe a teburi.