Bale:Har yanzu ban kai ganiyar wasana ba

Gareth Bale
Image caption Dan kwallon ya ce zai ci gaba da nuna kansa a wasanni

Dan kwallon Real Madrid Gareth Bale ya ce yanzu ya fara zura kwallaye a raga, duk da kwallaye uku da ya zura ranar Asabar.

Bale, mai shekaru 24,ya zura kwallo a raga da kai, sannan ya kara na biyu da kafar hagu, ya kuma kara na uku da kafar dama, sannan ya bai wa Karim Benzema kwallon da ya zura na hudu a raga, lokacin da suka casa Real Valladolid da ci 4-0.

Dan wasan ya sha fama da jinya, tun lokacin da ya koma Real Madrid lokacin da aka sayo shi daga Tottenham kan kudi kimanin fan Miliyon 85 a watan Satumba.

Tun lokacin da ya fara buga wasansa na farko a karawar da suka yi da Barcelona ya zura kwallo a wasan da aka lashe su da ci 2-1, tun daga lokacin Koci Ancelotti yake saka shi a wasanni har ma ya zura kwallaye takwas jumulla.