"Bama fargaba don an casa Barcelona"

Sergio Busquets
Image caption Dan wasan ya ce za su saka kaimi a sauran wasannin su

Dan wasan Barcelona Sergio Busquets ya ce guiwar 'yan wasan Barcelona ba ta yi sanyi ba saboda rashin nasarar wasanni biyu a jere.

Ranar Talata da ta gabata kungiyar tayi rashin nasara a hannun Ajax da ci 2-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai, sannan Athletico Bilbao ta lashe ta da ci daya mai ban haushi a ranar Lahadi.

Wasanni biyu da sabon koci Gerardo Martino kenan yayi rashin nasara a jere tun lokacin da ya zama kocin Barcelona a farkon kakar bana.

Barcelona tana matsayi na daya a teburin La-liga, duk da rashin nasarar da tayi a hannun Ajax ta sami kaiwa wasan sili biyu kwale a gasar cin kofin Zakarun Turai.