Wigan ta rabu da Kociyanta

Owen Coyle
Image caption Tafiyar Coyle ta kawo kociyoyi bakwai na Premier da na kasa da gasar sun rasa aiki a kwanaki bakwai da suka wuce

Kungiyar Wigan ta rabu da kociyanta Owen Coyle kasa da watanni shida bayan daukansa aiki.

Casa su da Derby ta yi da ci 3-1 ranar Lahadi shi ne rashin nasara karo na hudu a jere ga kungiyar ta 14 a gasar Championship ta Ingila.

Coyle tsohon kociyan Bolton ya maye gurbin Roberto Martinez a Wigan da burin dawo da kungiyar Premier bayan da ta fado Championship.

Kociyan mai shekaru 47 yayi nasarar wasanni bakwai ne kawai daga cikin 23 da ya jagoranci kungiyar.

Kungiyar ta Wigan ta ce sun raba gari da kociyan ne da amincewar juna bayan tattaunwa da shugaban klub din Dave Whelan.

Babban mai bayar da horo na kungiyar Graham da mataimakinsa Sandy Stewart su ne za su jagoranci kungiyar a wasanta da Leeds ranar Laraba.

Wigan tana da damar samun shiga matakin jerin kungiyoyi 32 na gasar Europa bayan da suka samu maki biyar a wasanninsu uku na rukuni.