Podolski zai dawo buga wasa

Lukas Podolski
Image caption Dan wasan yana sa ran idan ya dawo wasa ya ci gaba da zura kwallaye

Dan kwallon Arsenal mai buga wasan gaba Lukas Podolski zai dawo atisaye bayan kwashe watanni uku da yayi yana jinyar raunin da ya ji na tsagewar tsoka a cinyarsa.

Dan wasan ya ji raunin ne a lokacin da suka kara da Fenerbahce a gasar cin kofin zakarun Turai a karshen watan Agusta.

Tun kuma daga lokacin ne Olivier Giroud ya maye gurbin Podoski a wasannin Arsenal.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce dan wasan zai dawo atisaye ne dai bayan sun kara da Hull City a gobe laraba, kuma sai ya dauki sati guda yana atisaye kafin ya sami kuzarin bugawa kungiyar wasanni.