Fargabar mutuwa a filayen Premier

Amfani da kayan wasan wuta a filin wasa
Image caption Amfani da kayan wasan wuta a filin wasa

Ana fargabar cewa yawan amfani da bama baman hayaki da tartsatsin wuta a filayen wasa na gasar Premier ka iya janyo hadarin mutuwar mutane.

Wani bincike ya gano cewa ana amfani da kananan yara 'yan kusan shekara takwas wajen satar shiga da bama baman da kayan tartsatsin wutar filayen wasa.

Bincike ya nuna cewa kashi daya bisa uku na 'yan kallo sun taba gamuwa da matsalar abubuwan a filayen wasa kuma kashi 86 cikin dari sun damu da hatsarin da ke tattare da abubuwan.

Hukumomi sun bayyana cewa wani ka iya rasa ransa a sanadiyyar tayar da wadannan abubuwa a filin wasa.

A watanni uku na farko na kakar wasannin da ake ciki a gasar Premier da sauran wasanni na Ingila an samu matsalar kunna irin wadannan abubuwa har sau 96.

''Wannan ita ce babbar fargabar 'yan kallo a filayen wasa yanzu.'' in ji Cathy Long shugaban kula da jin dadin 'yan kallo na gasar Premier.

Karin bayani