Kofin Duniya: Ingila na fargaba

Kociyan Ingila Roy Hodgson
Image caption Ingila na iya kasancewa kasar da sauyin zai shafa

Ingila na fargabar kada a hada ta a rukunin da zai sa ta hadu da wata daga cikin fitattun kasashe a fagen kwallon kafa a gasar Kofin Duniya.

A ranar Juma'a ne a Brazil, hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Fifa za ta fitar da jadawalin wasannin gasar Kofin Duniya.

Sunan Ingila na cikin tukunya ta hudu ne(pot four) ta kashin kasashen da za a tsara hada wasan, inda take tare da wasu kasashen Turai takwas da ba sa cikin wadanda aka dauka na gaba gaba a kokari a kwallon kafa.

To sai dai yanzu Fifa ta ce za ta fitar da kasa daya daga cikin wannan tukunya da Ingila ke ciki ta mayar da ita tukunya ta biyu wadda ta kunshi kwararrun kasashe.

Za a yi hakan ne domin ganin an yi raba dai-dai a tsarin, saboda kasashe da ke baya a kwallon tara ne a tukunyar daga Turai, yayin da ake da bakwai irinsu a tukunya ta biyu.

Akan haka ne Ingila ta ke fatan kada wannan sauyi ya shafe ta, ta fada cikin rukunin kwararrun kasashen da za ta kasa kai labari a gasar.

Tukunya ta daya ta kunshi; Brazil d Spain d Argentina da Belgium da Colombi da Jamus da Switzerland da Uruguay

Tukunya ta biyu: Ivory Coast da Ghana da Najeriya da Aljeriya da Kamaru da Chile da Ecuador

Tukunya ta uku: Japan da Iran da Korea ta Kudu da Australia da Amurka da Mexico da Costa Rica da Honduras

Tukunya ta hudu: Bosnia-Hercegovina da Crotia da Ingila da Greece da Italiya da Netherlands da Portugal da Rasha da Faransa.

Karin bayani