''Ba mu dora wa Super Eagles buri ba''

'yan wasan Super Eagles na Najeriya
Image caption ''muna bukatar mu sama wa kungiyar yanayin da ya dace domin yin abin alfahari ga Afrika da 'yan Najeriya''

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya Aminu Maigari ya ce ba su sanya wa kungiyar wasan kasar wani buri ba a gasar Kofin Duniya ta 2014.

Duk da cewa a kwantiragin kocin kasar Stephen Keshi, an ambaci cewa akwai bukatar ya kai kasar matakin wasan gab da na kusa da karshe, shugaban ya nesanta kansa da hukumarsa daga hakan.

Maigari, ya kara da cewa, '' ba za ka iya hasashe ko gindaya wata bukata ko sharadi idan za ka je babbar gasa kamar ta Kofin Duniya ba.''

Ya ce, ''ina ganin ya fi dacewa ka bar kungiyar ta bi wasan daya bayan daya.''

An taba ruwaito mai tsaron gidan Najeriyar Vincent Enyeama na cewa Najeriya za ta iya daukar Kofin na Duniya.

Rabon da Najeriya ta ci wasa a gasar Kofin Duniya tun 1998 da ta yi nasara akan Bulgaria.

A lokacin ta tsallake matakin wasan rukuni-rukuni na gasar.

Kasashe uku ne kawai na Afrika suka taba zuwa matakin gab da na kusa da karshe na gasar Kofin Duniya.

A 1990 Kamaru sai Senegal a 2002 sai kuma Ghana a 2010.

Karin bayani