Sakamakon gasar Premier

Arsenal da Hull City
Image caption Arsenal ta ci gaba da jan ragamar Premier

A ci gaba da wasan gasar Premier sati na goma sha hudu an yi wasanni tara inda aka yi nasara a 8 daya kuma aka ta shi ba ci.

Ga yadda sakamakon wasannin ya kasance :

Arsenal 2 - 0 Hull City ,Liverpool 5 - 1 Norwich City

Man United 0 - 1 Everton ,Southampton 2 - 3 Aston Villa

Stoke City 0 - 0 Cardiff City , Sunderland 3 - 4 Chelsea

Swansea 3 - 0 Newcastle United ,Fulham 1 - 2 Tottenham

West Bromwich 2 - 3 Manchester City

Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a tebur da maki 34 sai Chelsea ta biyu da maki 30 sai Man City ta mai maki 28.

Man United daga ta takwas ta dawo ta tara da maki 22.

Sunderland tana ta karshe ta 20 da maki takwas yayin da Crystal Palace take gabanta ta 19 da maki 10.