Nasara ta bamu kwarin gwiwa - Pulis

Tony Pulis
Image caption Duk da wannan nasara Crystal Palace na cikin hadarin faduwa daga Premier

Tony Pulis ya samu nasara a wasansa na farko a matsayinsa na kocin Crystal Palace a kokarin kungiyar na kauce wa faduwa daga gasar Premier.

Marouane Chamakh ne ya ci kwallon, inda suka doke West Ham da ci daya me ban-haushi kuma kungiyar ta hau saman Sunderland a kasan teburin gasar Premier.

Pulis ya ce "sakamakon ya yi kyau mun samu maki uku da ya kara mana kwarin gwiwa.''

A wasanni 14 West Ham ce ta 15 da maki 13 ita kuma Crystal Palace tana ta 19 da maki 10.

Wassannin Crystal Palace da ke tafe;

- 7 Disamba: Cardiff (gida) - 14 Disamba: Chelsea (waje) - 21 Disamba: Newcastle (gida) - 26 Disamba: Aston Villa (waje) - 28 Disamba: Manchester City (waje)

Karin bayani