Moyes na sa ran tarbar girma

David Moyes
Image caption Yau ne kocin zai fara karawa da Eveton tun lokacin da ya bar kungiyar da ya horar shekaru 11

Kocin Manchester United David Moyes na sa ran tarbar girma daga magoya bayan Everton a karawar da za suyi a gasar Premier a yau, kuma karawar farko da zai yi da kungiyar tun lokacin da ya koma kocin United.

Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a filin Old Trafford a kakar wasan bana, bayan da ya share shekaru 11 yana jagorantar Everton.

Yau ne United za ta karbi bakuncin Everton a filin Old Trafford a gasar Premier wasan sati na 14

Sauran wasannin da za a kara a yau

Arsenal v Hull Liverpool v Norwich Southampton v Aston Villa Stoke v Cardiff Sunderland v Chelsea Swansea v Newcastle Fulham v Tottenham West Brom v Man City