Fifa ta roki jama'ar Brazil kan tarzoma

Masu zanga zanga a filin wasa a Brazil
Image caption Fifa na fargabar zanga zanga a lokacin gasar za ta kawo cikas

Babban sakataren Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ya roki 'yan kasar Brazil da ka da su yi zanga zanga a lokacin wasannin Kofin Duniya da za a yi a shekara mai zuwa.

Jerome Valcke ya ce gudanar da gasar a Brazil ya kasance da wahala sakamakon matsalar ayyukan gine ginen filayen wasa.

Da kuma zanga zangar da jama'a ke yi, yana mai kari da cewa bai dace ba a kawo wa gasar cikas.

An yi ta fama da tarzoma a kasar ta Brazil a kwanakin nan inda ake harar masu shirya gasar da wasunsu da ake zargi da bannata kudade akan gasar ta Kofin Duniya.

Karin bayani