Liverpool da Suarez sun dace-Rodgers

Luis Suarez
Image caption Tun bayan da ya gama jinya dan wasan sai zura kwallaye yake yi

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce kungiyar Liverpool ce ta fi dacewa da Luis Suarez, bayan da dan wasan ya zura kwallaye hudu a wasan da suka casa Norwich City da ci 5-1 a jiya Laraba.

Tun a baya Suarez ya so ya bar kungiyar a karshen kakar da ta wuce, amma daga baya ya sauya shawara kuma tun daga lokacin ya zura kwallaye 13 a wasanni goma da ya buga wa kungiyar a bana.

Rodgers ya ce dan wasan yana jin dadin wasa a kungiyar kuma cikin farinciki da walwala.

''Dukkan burin kungiyar sun dace da shi. Magoya bayan kungiyar na matukar kaunarsa, za ka iya ganin hakan da idanuwanka.''