Robben zai yi jinyar makwanni shida

Image caption Robben na taka rawar gani a Bayern Munich

Dan kwallon gefe na Bayern Munich Arjen Robben, zai yi jinyar makwanni shida saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.

Dan wasan na kasar Holland ya ji raunin ne a wasansu da kungiyar Augsburg na gasar kofin Jamus.

Saboda haka ba zai buga wasansu da Manchester City ba na gasar Zakarun Turai.

Robben mai shekaru 29, wanda tsohon dan kwallon Chelsea da Real Madrid ne, ya turgude ne bayan karonsa da golan Augsburg, Marwin Hitz.

Karin bayani