Ingila ba ta tsoron kowa in ji Hodgson

Roy Hodgson
Image caption Duk wanda aka hada mu da shi, shi ma zai iya jin tsoronmu

Kociyan Ingila Roy Hodgson ya jaddada cewa kasar ba ta tsoron haduwa da kowace kasa a hadin da za a yi na yadda kasashe za su fafata a gasar Kofin Duniya da za a tsara yau Juma'a.

Hodgson ya ce, '' zan mutunta tare da nuna sha'awa ga kowa, amma batun tsoro abu ne da babu shi a gabana.''

Hogson ya ce , ''sakona ga 'yan wasan da kasar shi ne ba za mu zo nan ba mu ji tsoron wani, za mu zo nan ne mu mutunta kowa. Mun san duk wanda za mu hadu da shi za mu iya nasara a kan shi kuma shi ma zai iya galaba a kanmu.''

Ingila na iya haduwa da Brazil ko Holland ko Italiya ko kuma Argentina a matakin rukuni na gasar da za a fara ranar 12 ga watan Yuni idan aka zabe ta a tukunya ta biyu (pot 2, wato inda ake tara sunayen kasashen da za a rika dauko wa ana tsara haduwar).

Za a fara zaman shirya jadawalin hada kasashen wasan ne a Bahia, Brazil da karfe hudu na yamma agogon GMT, biyar na yamma ke nan a Najeriya.