Mutuwar Mandela ta kankane taron Afrika

Hedikwatar AU
Image caption Mai yuwuwa shugabannin Afrikan da suke wurin taron su koma kasashensu su yi jimamin mutuwar Mandela.

Mutuwar Nelson Mandela ta kankane taron shugabannin Afrika da suka taru domin tattauna batun zaman lafiya da tsaro a nahiyar.

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya yi kira ga mahalatta taron da su karfafawa kasashen Afrika gwiwa domin samar da rundunar tsaro ta nahiyar.

Ana taron ne a lokacin da kasar Faransa take taka muhimmiyar rawa ta fannin aikin soji a Mali da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

A halin da ake ciki kasar Faransan ta tura karin dakaru domin aikin kare farar hula da kare rikicin addini a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Ministan tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce sojojin Faransa na sintiri a babban birnin kasar Bangui kuma wasu jirge masu saukr ungulu na kan hanyar zuwa kasar