Kofin FA: Arsenal da Tottenham

FA Cup
Image caption Za a ci gaba da fafatawa a wasannin zagaye na uku a kofin FA

Arsenal za ta kara da Tottenham a filin wasanta na Emirate a gasar kofin kalu bale na Ingila wasannin zagaye na uku.

Manchester United za ta karbi bakuncin Swansea City a filin Old Trafford, yayin da Norwich City da Fulham za su kece raini.

Chelsea za ta yi tattaki don karawa da Derby County, Blackburn Rovers kuma za ta karbi bakuncin Manchester City.

Sai kungiyar Kidderminster ta kara da Peterborough, a inda Macclesfield da Sheffield Wednesday su barje gumi.