Ana binciken Sodje kan cinikin wasa

Sam Sodje
Image caption Dan wasan ya nuna a shiye yake ya sayar da kowanne irin wasan kwallaon kafa ne

'Yan sanda suna tsare da mutane uku bayan da tsohon dan wasan Portsmouth ya sanar cewa ya taba shiga harkar sayar da wasan kwallon kafa.

An dauki hoton Sam Sodje a mujallar Sun ranar Lahadi lokacin da ya naushi dan wasa a fili a karawar kofin League One domin a ba shi jan kati shi kuma daga baya ya karbi ladan fan 70,000.

Ya kuma ce ya taba shirya wa da wani dan wasa akan kudi fan 30,000 domin a ba shi katin gargadi a wasan Championship.

A wani faifan bidiyo da aka dauka a boye, Sodje ya ce zai iya sayar da wasan Premier kuma a shirye yake ya kuma sayar da wasa a gasar cin kofin duniya da za a kara a badi.