An kama DJ Campbell saboda sayar da wasa

Image caption DJ Campbell

Tsohon dan kwallo a gasar Premier ta Ingila, DJ Campbell na daga cikin 'yan kwallo shida da 'yan sanda suka yi wa tambayoyi bisa zargin hannu a cinikin wasanni.

Mr Campbell wanda ke taka leda a kungiyar Blackburn, na daga cikin mutane shida da aka tsare a ranar Lahadi.

Matakin 'yan sandan ya biyo bayan hira da tsohon dan wasan Portsmouth Sam Sodje wanda ya ce, zai iya kitsawa da wani dan kwallo a bada katin gargadi ko na kora don a bashi kudi.

Hukumar binciken laifuka ta Birtaniya ta ce an bada belin mutane biyar a yammacin ranar Lahadi.

Kungiyar Portsmouth ta ce ta "kadu da takaici" a kan wannan zargin.

Dudley Junior Campbell mai shekaru 32 ya taka leda a kungiyoyin; Birmingham, Blackpool da kuma QPR.