Moyes ya dauki alhakin kayen kulab dinsa

David Moyes
Image caption kocin nasa ran kungiyarsa na daga cikin wacce za ta lashe kofin bana

Kocin Manchester United David Moyes ya dauki alhakin lashe kungiyarsa da Everton da Newcastle sukayi a jere, amma yana da tabbacin kungiyar za ta gyara kura-kuranta ta kuma yi fice.

United ta yi rashin nasara a wasanni biyu a jere a filinta na Old Trafford, kuma Arsenal da ke matsayi na daya a teburi ta bai wa United tazarar maki 13.

Moyes ya ce "Ran 'yan wasana a bace yake domin sun saba cinye wasanni, saboda haka za su farfado nan ba da dadewa ba.

"Ina son na tabbatar da 'yan wasan sun sake saka kaimi, da mai da hankali kamar yadda ya kamata."