CHAN: Super Eagles ta fara shiri

Super Eagles
Image caption Eagles ta fara atisayen gasar cin kofin nahiyar Afirka na 'yan wasa masu buga kwallo a gida

Tawagar Super Eagles ta Nigeria ta fara atisaye a katafaren filin wasa dake Abuja, domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 'yan kwallon dake wasa a Afrika.

Tun a ranar Litinin ne dukkan 'yan wasa 30 da aka gayyata suka halarci sansanin horon in banda Ejike Uzoenyi da yake fama da zazzabi aka kuma bashi damar ya huta kwana guda.

Atisayen da suka gudanar na tsawon sa'o'i biyu karkashin jagorancin mataimakan koci Daniel Amokaci da Hyoudonou Valere da Ike Shorunmo, sun yaba da yadda 'yan wasan suka nuna kwazo a filin atisaye.

Amokaci ya ce "Za a zabi hazukan 'yan wasa da za su wakilci kasa, kuma babu maganar son rai ko za bo dan lele, kowanne dan wasa ya kamata yasa hazaka domin nuna kansa.

Suma 'yan wasan zakarun kofin duniya ta matasa 'yan shekaru 17 da suka hada da Sunday Alampasu da Taiwo Awoniyi da Chigozie Agbin na daga cikin 'yan wasan da suka fara halartar sansanin horo da wuri.

A ranar Alhamis ne Stephen Keshi zai halarci sansanin horon Super Eagles din, domin ya halarci Brazil a lokacin da aka fidda jaddawalin kasashen da za su fafata a kofin duniya, ya kuma tsaye neman wurin da kungiyar za ta zauna a Brazil.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 'yan wasan gida ranar 11 ga watan Janairun shekara ta 2014 a Afrika ta Kudu.