"Har yanzu Ferguson na mulkar United"

Keane Ferguson
Image caption Tun a cikin shekarar 2005 suka sami sabani tsakani tsohon kyaftin da tsohon koci

Tsohon dan kwallon Manchester United Roy Keane ya ce har yanzu tsohon kocin kungiyar Sir Alex Ferguson ya na ta kokarin nuna tasirinsa a Old Trafford.

Ferguson wanda darekta ne a kungiyar a yanzu, bayan da yayi ritaya a watan Mayu daga horadda kungiyar da ya kwashe shekaru 26, kuma kocin Everton David Moyes ya maye gurbinsa.

Keane ya ce "koda yaushe yana da son mulki da nuna tasiri, har yanzu abinda yake ta kokarin yi kenan a kungiyar duk da ba shi ne Manajanta ba.

Keane ya bar kungiyar United ne a shekarar 2005 lokacin da ya sami rashin jituwa tsakaninsa da Ferguson.