Dan Man U ya kashe kansa a Kenya

Masoyan Manchester United
Image caption Manchester United na da dimbin masoya a fadin duniya

Wani dan Kenya da ya kasa daurewa rashin nasarar da Manchester United ta yi a karonta da Newcastle United ya hallaka kansa a karshen makon jiya, a cewar 'yan sanda.

Nasarar Newcastle a Old Trafford a karo na farko tun Fabrairun 1972 ta sa tazarar da ke tsakanin kungiyar da Arsenal mai jan ragama ta kai maki 13.

Kwamandan 'yan sandan Nairobi Benson Kibui ya ce; "John Macharia, mai shekaru 28 ya doka tsalle ne daga hawa na bakwai na wani gini da ke Pipeline Estate inda ya hallaka kansa saboda takaicin asarar 0-1 da United ta yi a hannun Newcastle."

Mutuwar ta Macharia ta yi daidai da ta wani magoyin bayan Arsenal a Kenya wanda ya kashe kansa a 2009. Suleiman Omondi mai shekaru 29 ya rataye kansa bayanda Manchester United ta lallasa Arsenal 3-1 a karawa ta biyu ta matakin kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Dangane da haka ne kwamandan 'yan sandan na Nairobi ya shawarci masu sha'awar kwallon kafa a Kenya da su rinka goyon bayan kungiyoyinsu na gida sababin kungiyoyin ketare da babu ruwansu da kasar.