'Kar a ragawa masu cinikin wasa'

match fixing
Image caption Ana ta samun yawan jama'a dake cinikin wasanni

Tsohon dan kwallon Ingila Alan Shearer ya ce ya kamata a dauki matakin ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu da hannu kan cinikin wasan kwallon kafa.

Mutane shida aka tsare ranar Lahadi bisa tuhumar cinikin wasa, an kuma bada belinsu, inda sai cikin watan Afrilu za a ci gaba da sauraren karar da aka shigar a kansu.

Shearer ya ce "Ba za ka iya kauda caca ba, amma za ka iya hana mutanen da suke da hannu a ciki, saboda haka duk wanda aka samu da hannu a ciki ya kamata a dauki matakin ba sani ba sabo."

Dan kwallon Blackburn DJ Cambell na daya daga cikin mutane shida da 'yan sanda suka yiwa tambayoyi dangane da cinikin wasannin kwallon kafa