UEFA: City ta lashe Munich da ci 3-2

Bayern Munich Man city
Image caption Da farkon wasan Munich ce ke rike kwallo kafin daga baya City ta lashe wasan

Manchester City ta lashe Bayern Munich mai rike da kofin bara har gida da ci 3-2 a gasar kofin zakarun Turai.

Nasarar da City ta samu ta takawa Munich burki na lashe wasanni 10 a jere a gasar, sai dai duk da rashin nasarar da kungiyar tayi, itace ta jagoranci rukuni na hudu a teburi sai City ta kare a matsayi na biyu.

Sauran sakamakon wasannin da aka fafata sun hada da

Man Utd 1 - 0 Shakhtar Donetsk Real Sociedad 0 - 1 Bayer Leverkusen FC Copenhagen 0 - 2 Real Madrid Benfica 2 - 1 Paris Saint Germain Olympiakos 3 - 1 Anderlecht Viktoria Plzen 2 - 1 CSKA Moscow

Karawa tsakanin Galatasaray da Juventus dakatar da wasan akayi sakamakon saukar dusar kankara.

Kungiyoyin da suka kai wasan siri biyu kwale sun hada da Man United da Bayer Leverkusen da Real Madrid da Paris Saint Germain da Olympiakos.