Sakamakon wasannin Zakarun Turai

Arsenal vs Napoli
Image caption Nasarar Borussia Dortmund da ta ci Marseille 2-1 ce ta fitar da Napoli ta ba Arsenal damar tsallakewa

Kungiyar Chelsea ta doke Steaua Bucharest da ci daya mai ban haushi a gasar kofin Zakarun Turai a karawar da suka yi a filin wasa na Stamford Bridge.

Dan wasan Chelsea Demba ba shi ne ya zura kwallo a raga a minti na 10 da fara wasa, kuma kungiyar ita ce a matsayi na daya a teburi sai Schalke a matsayi na biyu.

Arsenal rashin nasarar da ta yi a hannun Napoli da ci 2-0, dan wasan Napoli Higuin shi ne ya fara zura kwallo sai kuma Jose Callejon da ya zura kwallo ta biyu.

Duk da rashin nasarar da Arsenal ta yi ta samu kaiwa zagaye na gaba na kungiyoyi 16.

A sauran sakamakon wasannin

FC Schalke 04 2 - 0 Basel , Marseille 1 - 2 Borussia Dortmund

Atl├ętico Madrid 2 - 0 FC Porto , FK Austria Vienna 4 - 1 Zenit St Petersburg

Barcelona 6 - 1 Celtic , AC Milan 0 - 0 Ajax