Enyeama ya tsawaita kwantiragi da Lille

Vincent Enyeama
Image caption Golan ya ce jami'ai da magoya bayan kungiyar sun kara masa kwarin gwiwa

Mai tsaron ragar Super Eagles na Nijeriya Vincent Enyeama ya ce ya na son ya dade yana wasa a kungiyar Lille ta Faransa domin kungiyar ta kwanta masa a rai.

Enyeama ya sabunta kwantaraginsa ne da kungiyar na tsawon shekaru biyu ranar Litinin, bayan da dan wasan yake kan ganiyarsa musammam wasanni 11 da ya kara kwallo bata shiga ragarsa ba.

Tun lokacin da Lille ta fahimci kungiyoyi da dama na zawarcin dan wasan, abinda yasa ta hanzarta sabunta kwantaragi da dan wasa zuwa 2017.

Enyeama ya ce " Naji dadin tsintar kai na a kungiyar Lille, kuma shi yasa nake farincikin sabunta kwantaragi na da kungiyar."

Ya kara da ce wa "tun lokacin da na fuskanci 'yan wasa 'yan baiwa da muke wasa tare a kungiyar, na ga babu wani dalili da zai hana ni ci gaba da buga mata wasa."