Man U ta sha da kyar a wurin Shakhtar

Image caption Phil Jones ya kwato Manchester United

Phil Jones ne ya jefa kwallo daya tilo bayan hutun rabin lokaci, wacce ta bai wa Manchester United nasara kan Shakhtar Donetsk tare da zama zakarar rukunin A na gasar cin kofin zakarun Turai.

Da kyar da jibin goshi United ta samu wannan nasarar bayan da ta sha kaye a gida sau biyu a jere a karo na farko tun 2002.

Sau biyu Ashley Young na samun dama ya na bararwa.

Shigowar Robin van Persie da kuma kwallon da Phil Jones ya zura ce ta taimakawa United kaucewa abin kunyar shan kaye gida sau uku a jere a karo na farko tun 1962.