UEFA: Ronaldo yafi kowa zura kwallo

Cristiano Ronaldo
Image caption Dan wasan ana hasashen shine zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon bana

Cristiano Ronaldo ya zamo dan kwallo na farko da ya zura kwallaye tara a gasar Zakarun Turai a wasannin cikin rukunai, a lokacin da Real Madrid ta casa Copenhagen har gida.

Real ce ta daya a rukuni na biyu bayan da ta lashe wasanni biyar da buga canjaras a wasa guda. Dan wasanta Luka Modric shi ne ya fara zura kwallo a raga kafin Ronaldo ya zura kwallo ta biyu.

Ronaldo ya dawo bugawa Madrid wasa bayan da ya yi jinyar rauni da kuma dakatar da shi da aka yi wasa daya, yayinda Gareth Bale, dan kwallon da aka saya mafi tsada a kakar bana yayi fama da rashin lafiya.

Ronaldo mai shekaru 28, ya haura 'yan wasan da suka zura kwallaye takwas a baya da suka hada da Ruud van Nistelrooy a shekarar 2004-05 da Filippo Inzaghi da Hernan Crespo dukkanninsu da suka zura kwallayensu a shekarar 2002-03 da kuma Zlatan Ibrahimovic a shekarar 2013-14.