Blackburn ta baiwa DJ Campbel hutu

DJ Campbell
Image caption Dan wasan an bada belinsa sai watan Aprilu za a ci gaba da sauraron zargin da ake masa

Dan kwallon Blackburn Rovers DJ Campbell ba zai buga karawar da kulob din zai yi da Millwall ba a ranar Asabar, harma kungiyar ta dakatar da shi.

Dan wasan mai shekaru 32 yana daga cikin 'yan wasa shida da 'yan sanda su ka yiwa tambayoyi a kan cinikin wasan kwallon kafa.

Cambell ya koma Blackburn a watan Yuli. ya kuma bugawa kungiyar wasanni biyar izuwa yanzu.

Dan wasan ya buga wasan da kungiyar ta kara da QPR ranar 7 ga watan Decemba.