Klinsmann zai ci gaba da kocin Amurka

Jurgen Klinsmann
Image caption Kocin na fatan Amurka ta taka rawar gani a Brazil

Jurgen Klinsmann zai ci gaba da Horadda Amurka har sai bayan an kammala gasar kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a shekarar 2018.

Tsohon dan kwallon Jamus da ya lashe kofin a shekarar 1990, ya fara kocin Amurka a shekarar 2011, kuma ya jagoranci kasar shiga kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a badi.

Klinsman mai shekaru 49 ya jagoranci Jamus zuwa gasar kofin duniya ashekara 2006 a inda kasar ta kai wasan kusa dana karshe.

Kocin tsohon dan kwallon Tottenham da Stuttgart da Inter Milan, ya taba horadda Bayern Munich.