Honda zai koma Milan a Janairu

Keisuka Honda
Image caption Ana sa ran komawar dan wasan Milan ne a badi

Dan wasan Japan Keisuke Honda na shirin komawa AC Milan a farkon watan badi, bayan da kungiyarsa ta CSKA Moscow ta kasa kaiwa wasan kungiyoyi 16 na gasar cin kofin zakarun Turai.

Mataimakin shugaban kungiyar Adriano Galliani ya ce" A yanzu muna iya sanar da cewar daga ran 3 ga watan Janairu shekarar 2014, Keisuke Honda zai zama dan kwallon Milan.

Ya kara da ce wa "mun shirya rattaba kwantaragi a bangare guda, muna da ikon shedawa jama'a, amma abin da wahala saboda ba dan kwallon nahiyar Turai bane.

Dan wasan zai iya bugawa Milan wasa a karawar da za ta yi da Atlanta ranar 6 ga wata, ko karawar da za ta yi da Sassuolo